
A kowane zamani akwai wata fasaha da ke canza yadda mutane suke aiki,
koyo da kasuwanci. A zamaninmu, ita ce basirar wucin gadi (Artificial Intelligence, AI).
Da farko, bari in gaishe ka, mai karatu. Ina mika godiya ga wanda ya zaɓi ya karanta wannan aiki. Sunana Bilkisu Sabiu, kuma na rubuta wannan littafi ne
domin in taimaka wa al’umma su fahimci wata babbar fasaha da ke canza
duniya cikin sauri. Yayin da wasu suke jin tsoro ko shakka game da AI, ni na ga cewa akwai buƙatar jagora mai sauƙi, cikin Hausa, wadda za ta kawar da rudani
sannan ta nuna hanya mai amfani.
Fasahar AI ba wata sihiri ba ce, kuma ba abin tsoro ba ce kamar yadda wasu
suke zato. Ita ce kawai wata fasaha da ke iya yin wasu ayyuka da a da mutane ne
kawai suke iya yi — kamar rubutu, fassara, zanen hoto, yin lissafi da amsa
tambayoyi. Kamar kowace fasaha, amfaninta ya dogara da wanda yake amfani
da ita. Wuka a hannun likita tana ceto rai; wuka ɗaya a hannun mugu tana
lalata. Haka ma AI.
A cikin wannan littafi, ba za mu yi magana a kan fasaha kawai ba, za mu koyi
yadda ake amfani da ita a aikace. Za mu fara daga fahimtar menene AI,
sannan mu kalli kayan aiki daban-daban da suke akwai, mu koyi yadda ake yin
magana da su (prompt), sannan mu ga yadda za a yi amfani da su wajen samun Fasahar AI — Jagora ta Aiki
kuɗi da bunƙasa kasuwanci. A ƙarshe, za mu tattauna da’a, aminci da amfani mai kyau.
WA YA KAMATA YA KARANTA WANNAN LITTAFI
* Ɗalibai da malamai da ke son koyo da koyarwa cikin sauki.
* ’Yan kasuwa ƙanana da matsakaita da ke son bunƙasa tallacetallace.
* Marubuta, masu ƙirƙira da masu bayar da abun ciki (content).
* Duk wanda yake son ya fara amfani da AI amma bai san ta inda zai fara ba.
Buy More @
General Store link
https://selar.com/m/bilkisusabiu