Huruf, Tajweed da Nahwu (Harda English)
External Access

Huruf, Tajweed da Nahwu (Harda English)

(0 Ratings)
1
โ‚ฆ10,000.00โ‚ฆ15,000


โ˜๐Ÿพโ˜๐Ÿพโ˜๐Ÿพ


Yadda Zaka Iya Karatun Arabiyya, Sanin Ilimin Tajweedi da Nahwun Larabci ta Wayarka


Idan kana wani abu ne sai ka tsaya ka ji wannan zancen Kafin a goge shi ๐Ÿ›‘๐Ÿ›‘๐Ÿ›‘


Ko shin ka taba jin labarin Makahon yaro da ya haddace alQurani ya rike lambar kowanni ayah?


Wannan shine Jihad Al-Maaliki, Makahon yaro Dan shekaru 15 da ya haddace Qurani ayah ayah.



To Amma Ba batun Jihad muke ba, BATUN BABBAR JIHADI muke wato nemar ilimi.


Idan wannan yaron yayi haka mu wani hujja zamu Bada wa Allah na rashin memar ilimi?


A yau Muna da wayoyin hannu masu kwakwalwa Amma ba mu amfanin da su yadda ta dace, sai dai Bata lokutan mu!


Mun manta ilimi shine ginshiki na rayuwa Kuma da shi ake rike al-umma. Dashi Annabin tsira zai yi alfahari!


Ta iya yiwuwa ka taso da sha'awar ilimin Amma;


โœ”๏ธ Babu Mai biya Maka ko daukar nauyi

โœ”๏ธ Kila ka bari kasuwa ta shagaltar da kai

โœ”๏ธ Kila Kuma Boko ta shagaltar da kai


Ashe ba zan nuna Maka abunda ya Fi kasuwanci Fa'ida ba?


Ashe ba zan nuna Maka abin da yafi Boko amfani ba?


Ilimi musamman wanda ya shafe addinin ka!!


โœ”๏ธ Mai ilimi, ilimi ke kare shi


โœ”๏ธ Mai ilimi magajin annabawa ne


โœ”๏ธ Mai ilimi mutuntashi Ake cikin Jama'a


โœ”๏ธ Idan ka yi ka karantar ta zamo maka Sadaka jariya bayan mutuwa


โœ”๏ธ Sannan tan iya zama hanyar cin abincin ka na halas


Ba'a makara ko girma da Neman ilimi, (daga tsumma zuwa makara).


To Wai Ya Abun Yake Ne Malam???



Shin idan an Bude makaranta a waya yadda Zaka iya shiga kayi karatu online ko offline a wayarka ba zaka shiga ba?


To ka Bari na gabatar Maka da Madrasa Hausa! ๐Ÿ›‘


Madrasa Hausa Makaranta ce ta musamman Mai rajista da Government wacce Ake Bude ta a Telegram don


โœ”๏ธ Dalibai Maza da Mata


โœ”๏ธMatasa da manya


โœ”๏ธDalibai da Yan Kasuwa


โœ”๏ธWanda ya taba da Wanda Bai taba karatu ba.


Me Da Me Muke Karantarwa Kuwa?


โœ… Huruf da Hada Baki


Muna koyar da yadda Zaka iya hada Baki har ka iya Karatun larabci da rubutu!


Mun tanadi bidiyoyin karatu, ayyuka da ma matakin wasa kwakwalwa ga Dalibai kullum duniya


Muna da Dalibai sama da mutum 150 a yanzu haka a ajin hada Baki, Kuma da yawa sun iya bayan shigan su Ajin namu.


โœ… Tajweedi na Al-Qurani


Tajweedi shi ne ilimin Kyautata Karatun Alquran mai girma. A gurguje ga kadan daga bayananta


Tajweedi shi zai sa kasan nau'ukan harufa da mafitansu


Tajweedi shi zai sanar da Kai amfanin wasula da wasu dige-dige


Tajweedi ne zai sanar da Kai inda ya kamata a tsaya, da inda ba a son tsayawa a karatu


Ilimin Tajweedi ilimi ne da zai taimaki mutum ya samu kusanci zuwa ga Allah ta hanyar karanta Qur'ani daidai


โœ… Ilimin Nahwu


Ko shin ka taba ganin wani ya karanta Kalmomin larabci alhalin ba wasula a kansu? Wannan ilimin Nahwu ne ke aiki!


Ilimin Nahwu shi zai koya Maka Gina zance daidai a larabci


Ilimin Nahwu shi zai koya Maka larbaci da sanin asalin ma'anonin Kalmomi a larabci.


โœ… English (Bonus)


Wannan Kyauta ne Muka Kara muku ita, Kuma wannan Ajin zai koyar da turanci da yadda Zaka gyara rubutunka (handwriting)


Karatunmu kuwa game da kowanni aji Muna farawa ne ta kasa-kasa saboda wadanda Basu taba karatu ba.



A Wata Kafa Ake Karatun, Yaya Tsarin?


Muna Karatun a Telegram ne, duka Ajin uku har da Kyautar Ajin English!


Da zarar Dalibi yayi rajista muke Bashi link Wanda zata kaishi inda zai shiga ajin duka.


Idan ya shiga kowanne daga Ajin akwai bidiyoyin ajin a liqe yadda Zaka iya sauke su duka ka musu folder a wayarka ka rika kallo ko ba data.


Idan ka Gamu da aiki a yayin kallon wani bidiyo, yin aikin zaka yi ko da waya ko a takarda sai ma day hoton aikin ka turo a ajin.


Haka idan kana da wata tambaya har yanzu, Ajin zaka kawo na amsa Maka ita ko wakilaina.


Yaushe Da Yaushe Ake Karatun?


Babu wani lokacin musammsan na karatu, abun sani bidiyoyin duka da lambobi da sunan abin da aka Yi a kansa.


Saboda haka, ko wani lokacin kaga dama zaka yi karatu.


Mun tsara haka ne saboda idan muke ce ga lokacin karatu, Kila lokacin sana'arka ce, kenan Za'a bar wani a Baya!



To Yaya Idan an Yi Nisa an Barni?


A ko yaushe ka shiga Babu damuwa, zaka ga bidiyo a sama, Wanda da ka taba shi zai Kai ka bidiyon farko.


Bidiyoyin Huruf sun Kai Sha bakwai, Nahwu Talatin da Kari, Tajweedi ma haka.



Nawa Ake Biya Don Shiga???


Duk abinda Muka ce a biya don shiga ajin yayi. Misali:


Ajin Huruf = N20,000

Tajweedi = N20,000

Ajin Nahwu = N30,000


Duka = 70,000


Amma ku kwantar da hankalinku, Baku biyan dubu saba'in, Baku biyan hamsin.


Dubu Goma kawai zaka biya (N10,000) Kuma sau Daya rak ake biya


Kuma Muna Bada Certificate idan Dalibi ya kammala Ajin Muka jarabce shi

Frequently bought together

ยฉ 2026 Umar Bappa. All Rights Reserved.

Powered By