ACTIVE WORD POWER (AWP)
External Access

ACTIVE WORD POWER (AWP)

(0 Ratings)
1
$3.00$3.69

Wannan kwas ɗin Active Word Power an tsara shi ne domin masu koyon Turanci matakin tsakiya (Intermediate).


Zai taimaka wajen koyo da fahimtar kalmomin Turanci musamman waɗanda aka fi amfani da su don yin magana a rayuwar yau da kullum.


Za ka fahimci ma'anar su, yadda ake furta su, da kuma yadda ake amfani da su cikin sauƙi da sauri.


Manufar kwas ɗin ita ce:


  • Sauƙaƙa koyon kalmomin Turanci


  • Koya yadda ake amfani da su


  • Nuna hanyar koyo mafi dacewa



Kwas ɗin Ya Kunshi


1. Darussa masu sauƙin fahimta


  • Ana gabatar da su ta hanyar bidiyo da ke ɗauke da bayani mai sauki kuma mai ma’ana


2. A cikin kowanne darasi


  • Za ka koyi kalmomi guda uku


  • Ga kowacce kalma, misalai uku


  • Kenan duk darasi, misalai tara


3. Ga kowacce kalma

Akwai kulawa ta musamman a kan:


  • Ma’ana (Meaning)

Don fahimtar ainihin ma’anar kalma


  • Furuci (Pronunciation)

Don fahimtar yadda ake furtawa dai-dai


  • Lokacin Amfani (Tense)

Don fahimtar yadda kalmar ke iya sauyawa a lokuta daban-daban


  • Misalai (Examples)

Don sabawa da amfani da kalmar a cikin magana



Gudanar da Darasi


  • Za a ba ka darasi daya kowacce rana


  • Har zuwa wata daya, kwanaki talatin


  • Gaba daya kalmomi 90, misalai 270



Amfanin Wannan Kwas


  • Za ka koyi kalmomi masu amfani a rayuwar yau da kullum


  • Za ka inganta Turancin ka cikin sauri da sauki


  • Za ka saba da tsarin koyo mafi dacewa


  • Za ka samu kwarin gwiwar yin Turanci



Karin Fa’idodi


Za ka shiga group a WhatsApp domin:


  • Yin tambayoyi a koyaushe


  • Tattaunawa da sauran ɗalibai


  • Samun ƙarin taimako daga malami



Wane ne Ya Dace da Wannan Kwas din?


  • Mai koyon Turanci matakin tsakiya


  • Wanda yake son inganta Turancin sa


  • Wanda ya ke son yin bitar muhimman kalmomi


Active Word Power ba kawai kwas bane, hanya ce mai sauƙi da inganci wadda za ta taimaka maka wajen koyon muhimman kalmomin Turanci ba tare da shan wahala ba.


Idan kana son inganta Turancin ka ta hanyar koyon kalmomi da kuma yadda ake amfani da su cikin sauƙi, wannan kwas ɗin naka ne. Ka tabbata ka yi mana magana ta WhatsApp. Sai mun hadu a aji!

Frequently bought together

© 2026 Keen Deeny Academy. All Rights Reserved.

Powered By