
NAZARIN HALAYYAR DAN
littafi ne da ke zurfafa bincike kan yadda ɗan adam ke tunani, ji da ɗabi’a.
Littafin yana bayani kan hanyoyin da ake bi wajen fahimtar halaye, da abubuwan da ke tasiri a kai – kamar muhalli, kwarewa, ilimi, da al’adu.
Haka kuma, ya ƙunshi bayanai kan manufofi, hanyoyin bincike, da kalubalen da masana ke fuskanta wajen nazarin ɗabi'un mutane.
Ana amfani da wannan littafi musamman a fannin ilimin halayyar ɗan adam (psychology), don ilmantar da ɗalibai da masu bincike kan ɗabi’a da halayen jama’a.