
Wannan kwas ɗin Conversational English Simplified an tsara shi ne domin masu koyon Turanci matakin tsakiya (Intermediate).
Zai taimaka wajen koyo da fahimtar kalmomin Turanci musamman waɗanda aka fi amfani da su don yin magana a rayuwar yau da kullum.
Za ka fahimci ma'anar su, yadda ake furta su, da kuma yadda ake amfani da su cikin sauƙi da sauri.
Akwai kulawa ta musamman a kan:
Don fahimtar ainihin ma’anar kalma
Don fahimtar yadda ake furtawa dai-dai
Don fahimtar yadda kalmar ke iya sauyawa a lokuta daban-daban
Don sabawa da amfani da kalmar a cikin magana
Za ka shiga group a WhatsApp domin:
Conversational English Simplified ba kawai kwas bane, hanya ce mai sauƙi da inganci wadda za ta taimaka maka wajen koyon muhimman kalmomin Turanci ba tare da shan wahala ba.
Idan kana son inganta Turancin ka ta hanyar koyon kalmomi da kuma yadda ake amfani da su cikin sauƙi, wannan kwas ɗin naka ne. Ka tabbata ka yi mana magana ta WhatsApp. Sai mun hadu a aji!