
A zamanin yau da duniya ta koma dijital, yana da matuƙar muhimmanci ga mutum ya mallaki ilimin da zai ba shi damar samun kuɗi ba tare da dogaro da wuri ko lokaci ba. Wannan littafi ya zo ne don taimakawa kowane ɗan Adam – matashi ko babba, namiji ko mace – da hanyoyi 50 da mutum zai iya amfani da wayar hannu ko kwamfuta domin fara samun halal ɗin kuɗinsa daga gida ko ko'ina.
Mun tsara hanyoyin ne ta yadda kowanne daga cikinsu ya zo da:
1.Bayani dalla-dalla (menene?)
2. Abubuwan da ake buƙata
3. Matakan farawa (Free & Pro)
4. Hanyoyin samun kuɗi
5. Dabarun cin nasara
6. Misalai da Links masu amfani
Ko kai sabo ne a harkar intanet, ko kuma kana da ɗan ƙwarewa, wannan littafi zai baka kwarin gwiwa da tsarin da zaka bi wajen gina hanyarka ta samun kuɗi mai ɗorewa ta hanyar zamani.