Wannan littafin mai suna “Matakan Nasara a Trading ” na
rubuta shi ne don fayyace hanyoyin da za ka bi don kasancewa
a cikin jerin 10% na 'Successful Traders'. Za ka ga dalilin da
yasa 90% suke rashin nasara, sannan ka ga dalilin da ya sa 10%
ɗin suka yi suka samu nasara wanda in har ka yi amfani da
koyarwar da ke cikin wannan littafin in sha Allah za ka ga canji
a cikin 'trading career' naka, ko ince in sha Allah za ka canza
daga mai fafutukar da babu riba (struggling unprofitable trader)
zuwa ga wanda ya yi nasara yake samun riba (successful
profitable trader).
Da fari kafin mu shiga cikin wannan littafin, zan janyo hankalin
mai karatu, cewa wannan littafin ba kamar sauran littatafan
'trading pshycology' ba ne, ya sha bamban, ta warare da dama.
Ba wai za ku yi karo da sanannun abubuwa ba ne da kuka saba
ji, mafi akasarin abin da ke ƙunshe a wannan littafin ƙwarewa
ce (experience) ce, da kuma dabaru na musamman (personal
approach) irin wanda ya yi mun aiki, da kuma ɗalibai nawa
wajen mayar da ni 'consistently profitable trader'.
Abu na gaba shi ne, duk da littafin an rubuta shi ne da Hausa,
Akwai kalmomin turanci da dama da ban fassara su ba zuwa
Hausa, na yi hakan ne a sane don ina ganin barin su a Turanci
ne zai fi bani damar bayyana kaina da kyau yadda mai karatu
zai fi tsintar bayanan da ke cikin littafin yadda ya dace.