
A wannan kwas ɗin za ka koyi mataki-mataki yadda ake sauya ko sake samun muhimman takardu idan sun ɓace, sun lalace ko aka sace su. Za a yi bayani dalla-dalla kan yadda ake maye gurbin:
Katin Ɗan Ƙasa (National ID)
Lambar NIN
BVN
Katin Zaɓe (PVC)
ATM Card
Fasfo (International Passport)
Lasisin Tuƙi (Driver's License)
Takardun banki da sauran muhimman takardu
An shirya wannan kwas ne cikin sauƙi domin kowa ya fahimta, tare da bayanin matakan da za a bi, inda za a je, da abubuwan da ake buƙata domin kammala aikin cikin nasara.
